Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Ya Rasu a London

 

Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Ya Rasu a London

Abuja – 13 Yuli, 2025 | TEC News

Tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Muhammadu Buhari, GCFR, ya rasu yau da rana a wani asibiti da ke birnin London, ƙasar Birtaniya.

 

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Garba Shehu, wanda ya sanya hannu a madadin iyalan marigayin, inda ya tabbatar da rasuwar shugaban a safiyar yau.

 

“A cikin alhini da jimami, iyalan tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, GCFR, na sanar da rasuwarsa yau a wani asibiti da ke birnin London. Muna roƙon Allah Madaukaki Ya jikansa, Ya gafarta masa, kuma Ya saka masa da Aljannatul Firdaus. Ameen,” in ji sanarwar.

 

Shugaba Buhari, wanda soja ne mai ritaya kuma tsohon shugaban mulkin soja daga 1983 zuwa 1985, ya sake dawowa ne a 2015 a matsayin shugaban da aka zaɓa ta dimokuraɗiyya, kuma aka sake zaɓensa a 2019 har ya kammala mulkinsa a 2023.

 

Har yanzu ba a bayyana cikakken bayani kan shirye-shiryen jana’izar sa ba.

 

 

Comments (0)
Add Comment